Gwamnatin Tinubu ta tabbatar da shirin ta na kara harajin siyan kayayyaki (VAT)

0
68

Gwamnatin Tinubu ta tabbatar da shirin ta na kara harajin siyan kayayyaki wanda aka fi sani da (VAT) a turance.

Ministan kudi na Nigeria, Wale Edun, Ne ya bayyana hakan lokacin da yake yin bayani a wajen wani taron masu zuba hannun jari wanda bankin duniya da asusun bayar da lamuni na duniya IMF, suka shirya a birnin Washington DC, na Amurka.

Karanta karin wasu labaran:Yan ta’adda sun kakabawa al’ummar Katsina biyan harajin dole

Yace karin harajin zai shafi manyan kayan da ake siyarwa.

Wale, yace za’a rika kara harajin da kadan-kadan bayan majalisar dokokin kasa ta amince da karin.

Sai dai yace ba za’a saka harajin akan kayayyakin da talakawa ke ta’ammali da su ba.

A watan Satumba shugaban wani kwamitin tsare tsaren kudi da shugaban Nigeria Tinubu, ya kafa, Taiwo Oyedele, ya nemi majalisar kasa ta amince da karin VAT daga kaso 7.5 cikin dari zuwa kaso 10.

Duk da gwamnatin tace zata cire kayayyakin da talakawa ke amfani da su daga karin harajin amma ana zaton dole hakan zai kara matsalar hauhawar farashin kayan masarufi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here