Nigeria zata ciyo bashi saboda siyo jiragen yaki

0
55
Sojin sama

Gwamnatin tarayya ta amince da karbo rancen sama da dala miliyan 600 domin sayen wasu jiragen yaki samfurin M-346.

Gwamnatin na burin samar da jiragen ga rundunar sojin sama domin kai hare-hare ga yan ta’adda a farkon shekarar 2025.

A yanzu dai Kasar nan ta kara yawan kudaden da take kashewa a fannin tsaro yayin da take yaki da ‘yan bindiga tsawon shekaru musamman a arewa.

Karanta karin wasu labaran:Sojojin Nigeria biyar sun mutu a hatsarin mota 

Group Kaftin Saddiq Shehu wani masanin tsaro ya ce duk da wannan yunkuri na gwamnati na siyen wadannan jirage, har yanzu sojojin bukatar kayan aiki.

Ya ce, babbar mastalar da kayan aikin sojin ke fuskanta ita ce rashin iya gyara su, mussaman jirgin saman, wanda idan ya samu wata matsala ba a iya gyara su a nan, haka ne ke tilasta wa gwamnati siyo wani sabo, maimakon a gyara wanda ake da su.

Haka kuma ya ce siyo jirgin zai bayar da gudunmawa wajen magance ayyukan Boko Haram da Yan fashin daji ba.

A cewarsa wannan jirgi, ana iya amfani da shi wajen harbo abu daga sama zuwa kasa, sannan za a iya amfani da shi wajen bayar da horo ga wadan da za su tuka jirgin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here