Al’ummar Katsina sun fara kare kansu daga harin yan ta’adda

0
44

Gwamnan jihar Katsina Dr. Dikko Umar Radda ya ce an fara samun nasara kan kiran da suke yi wa jama’ar jihar na tashi tsaye wajen kare kansu daga harin ‘yan bindiga.

Gwamna Dikko Umar,  ya ce kawo yanzu akwai garuruwa da dama da ‘yan bindigar basa sha’awar shiga, saboda matakan kare kai da mazaunan yankunan suka dauka.

Karanta karin wasu labaran:Yan ta’adda sun kakabawa al’ummar Katsina biyan harajin dole

Ya ce ba wai suna kira ga al’umma su tashi su dauki makami ba ne, sai dai don su kare kansu, saboda jam’an tsaron da ake da su a Najeriya ba za su iya kare mutane ba.

Radda ya ce abun da suka umarci mutane shi ne bayar da matasa a basu horo, da abubuwan da zasu iya bayar da tsaro ga kawunansu, kafin jami’an tsaro su kawo musu dauki in aka samu kai hari.

Sai dai wasu na ganin cewar a duk lokacin da gwamantoci suka fara kiran jama’a su fara kare kansu, tamkar sun gaza sauke nauyin dake kansu ne.

Amman gwamnan ya ce  ba haka lamarin yake a wajensu ba, kawai dai jami’an tsaro sunyi kadan a Nigeria.

Jihar Katsina na daga cikin jihohin arewacin Nigeria masu fama da matsanancin rashin tsaro, da aka gaza magancewa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here