Gwamnatin Kano ta takaita zirga zirga saboda zaben kananun hukumomi

0
65

Gwamnatin Kano ta saka dokar hana zirga zirga ta tsawon awanni 18 daga karfe 12:00 na daren Juma’a zuwa 6:00 na yammacin ranar Asabar.A wata sanarwa da kwamishinan labarai Malam Halilu Ɗantiye, ya fitar gwamnatin ta ce ta dauki matakin hakan bayan tattaunawa da jami’an tsaro na jihar.Sanarwar ta kara da cewa dokar hana zirga zirgar ta shafi daidaikun jama’a da ababan hawa a daukacin kananun hukumomin jihar 44.Dokar ta ware mutanen da suke aikin zabe da sauran masu ayyukan bukata ta yau da kullum, da cewa babu su a cikin dokar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here