Shugaban kasa Bola Tinubu ya nemi jami’an tsaron da ke yaki da ‘yan bindiga a yankin arewa maso yamma su kawo karshen matsalar tsaro nan ba da jimawa ba.
Ministan tsaro Muhammad Badaru Abubakar ne ya bayyana haka lokacin wata ziyara da ya kai shalkwatar rundunar Operation Fansar Yamma mai yaki da ‘yan bindiga a Zamfara.
Karanta karin wasu labaran:Dattawan arewa sun ce shugaba Tinubu yana Kokarin magance rashin tsaro a yankin
Badaru ya ce shugaba Tinubu yayi matukar damuwa da matsalar rashin tsaro da jihar zamfara ke fuskanta, kuma ya umarci sojoji su kawo karshen matsalar a yankin arewa maso yamma baki daya.
A lokacin ziyarar ministan ya yaba da irin tsare tsaren sojojin na naki da ‘yan bindigar tare da umartarsu su ci gaba da farautar manyan shugabannin ‘yan bindigar yankin.
Ministan ya kuma ziyarci gidan gwamnatin jihar, Zamfara inda ya tattauna da gwamnan jihar kan batutuwan da suka shafi tsaro a faÉ—in jihar.