Sanatocin Arewa sun nemi a gaggauta gyara wutar lantarkin yankin

0
88

Kungiyar Sanatocin Arewa ta bukaci gwamnatin gwamnatin tarayya ta gaggauta dawo da wutar lantarki a jihohin Kano, Kaduna, Katsina, Jigawa da sauran jihohin Arewa.

Sanatocin sun bukaci gwamnatin ta gaggauta gyara layukan samar da wutar dake Shiroro zuwa Kaduna domin dawo da wutar.

Sanarwar da Shugaban kungiyar Sanatocin Arewa, Sanata Abdulaziz Yar’adua ya sanya wa hannu bayan ganawar da suka yi ranar Asabar a Abuja, ta kuma bukaci gwamnati ta aiwatar da matakan dakile lalata kayayyakin lantarkin a Arewa.

Wasu sassan Arewa na cikin duhu, biyo bayan wata matsalar da aka samu a layin wutar lantarki mai karfin 330kV data kawo wuta arewa.

Lamarin dai ya haifar da katsewar wutar lantarki a yankin Arewa maso Gabas, Arewa maso Yamma da kuma wasu sassan Arewa ta Tsakiya.

Sanarwar ta ce harkokin kasuwanci sun tsaya a sakamakon matsalar lantarkin da ake fuskanta wanda ya jefa tattalin arziki cikin wani hali da tabarbarewar harkokin kiwon lafiya.

Kamfanin rarraba lantarki na kasa TCN ya sanar da cewa za’a dauki dogon lokaci kafin gyaran wutar saboda matsalar tsaro.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here