Sojan Nigeria ya harbe abokin aikin sa har lahira

0
62

Wani jami’in sojan ruwa na Nigeria ya bindige abokin aikin sa Soja, har lahira a jihar Katsina.

Lamarin ya faru ranar juma’ar data gabata.

Jami’in yada labarai na rundunar sojin ruwa ta Nigeria Edward Buba, yace sojan ya kashe dan uwan sa lokacin da ya bude wuta kan mai uwa da wabi.

Buba, yace tuni aka kama tare da tsare wanda yayi kisan mai suna Seaman Akila A. wanda zuwa yanzu an fara gudanar da bincike akan sa.

Shalkwatar tsaron kasa tace akwai ayar tambaya akan Wannan danyen aikin da Seaman Akila, ya aikata.

Haka zalika Edward, ya ce bayan gudanar da bincike za’a gurfanar da wanda ake zargi a gaban kotun hukunta sojoji don yi masa hukunci.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here