A ranar litinin mai zuwa wa’adin da babban ministan birnin tarayya Abuja Nyesom Wike, ya bai wa mabarata na daina bara a titunan babban birnin zai cika.
Kafin cikar wa’adin kungiyar masu bukata ta musamman da ke arewacin kasar nan ta yi kira ga yayan ta da su tashi da azumi a ranar don neman Allah ya kawo masu dauki.
Kungiyar ta kuma nemi masu ruwa da tsaki tun daga kan yan majalisar wakilai, da sanatoci da sarakunan da sauran mahukunta su shiga lamarin don taimaka musu.
Shugaban kungiyar masu bukata ta musamman na arewacin Najeriya Yarima Sulaiman Ibrahim, ya shaida wa BBC cewar, ya kamata ministan birnin tarayya Abuja, ya sake shawara, duk da cewar abun da ministan ya fada doka ne kuma ba za su hana doka aikin ta ba, sai dai babbar matsalar ita ce ministan ya ce akwai wadanda ke sajewa da jama’a suna bayar da bayanan sirri ga bata-gari a cikin almajiran.
A cewar sa bukatar su itace a duba wacce dama dokar kasa ta ba su, sannan a kira su a tattauna da su don jin matsalolin da suke ciki.
Yarima yace ta haka ne za’a samar da mafitar da zata hana yin bara.
Haka kuma ya ce babban abin da suka fi bukata shi ne a saurare su aji koken da suke da shi, a magance musu.
Haka kuma ya ce akwai dokar da tsohon shugaban kasa Buhari ya saka wa hannu kan masu bukata ta musamman, inda aka ware kashi 5 cikin dari zuwa sama ga masu bukata ta musamman a kowacce ma’aikata, don basu aiki amma ba a aiwatar da hakan.