Amurkawa miliyan 41 sun kada kuri’a a zaben shugaban kasar dake tafe a watan Nuwamba

0
64

Zuwa yanzu fiye da Amurkawa miliyan 41 ne suka zabi shugaban kasa ta internet gabanin gudanar da zaben na zahiri a ranar 5 ga wata mai kamawa wato Nuwamba.

Amurkawan sun kada kuri’ar tasu ta manhajar aikewa da sakonni ta Email.

Karanta karin wasu labaran:Donald Trump ya sha alwashin korar baki daga Amurka

Duk da cewa wannan ba shine zai nuna yanayin da zaben zai kasance ba, amma ana kyautata zaton za’a samu fitowar masu kada kuri’a a lokacin zaben na zahiri a ranar 5 ga Nuwamba.

Idan aka yi la’akari da tarihi magoya bayan jam’iyyar Democrats sun fi kada kuri’a ta email yayin da magoya bayan Republican suke fi mayar da hankali a lokacin yin zaben zahiri.

A shekarar 2020 mutane miliyan 2 da dubu dari 7 ne suka kada kuri’ar su a internet a jihar Georgia, wanda hakan ya taimakawa shugaban Amurka na yanzu Joe Biden, har ya samu nasara akan tsohon shugaban kasar Donald Trump.

Magoya bayan jam’iyyar Republican sun ayyana zaben internet a matsayin magudi.

Yar takarar shugabancin Amurka karkashin jam’iyyar Democrats Kamala Harris, ta nemi magoya bayan ta suyi amfani da damar yin zabe ta internet, lokacin da take yakin neman zabe.

Tsohon shugaban Amurka Donald Trump, shine ke yiwa jam’iyyar Republican takara sai mataimakiyar shugaban kasar ta yanzu Kamala Harris, dake yiwa jam’iyyar Democrats takara.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here