Kwankwaso ya nemi jihohi su samarwa kansu wutar lantarki

0
64
Rabiu-Musa-Kwankwaso-
Rabiu-Musa-Kwankwaso-

Dan takarar shugaban kasa na Jam’iyyar NNPP a zaben 2023, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya bayyana amfanin dake tattare da jihohi su fara samar wa kansu da kansu wutar lantarki.

Karanta karin wasu labaran:Sanatocin Arewa sun nemi a gaggauta gyara wutar lantarkin yankin

Kwankwaso ya sanar da hakan a matsayin tsokacinsa kan lalacewar wutar da ta jefa yankin Arewa cikin rashin wutar fiye da mako daya.

Ya ce, abin takaici ne yadda akasarin yankin Arewa ke cikin duhu sakamakon lalata layin wutar lantarki mai karfin 330kV da ke dauko wutar lantarki daga Shiroro zuwa Kaduna da ke kai wutar zuwa Kano da Kaduna da kuma wani layin da ke kai wutar zuwa jihohin Bauchi da Gombe da sauran yankin Arewa ta tsakiya.

Wannan matsalar ta jefa iyalai da masana’antu cikin duhu.

Yace tsawon lokacin da aka dauka ba tare da gyara wutar ba ya nuna irin gazawar bangaren wutar lantarki wanda ke bukatar a magance domin hana aukuwar haka a nan gaba.

Idan za’a iya tunawa kamfanin rarraba lantarki na kasa TCN yace rashin tsaro ne zai hana gudanar da gyaran lantarkin yankin Arewa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here