Shugaba Tinubu ya gana da ministan lantarki saboda lalacewar wutar arewa

0
65

Ministan wutar lantarki Adebayo Adelabu ya bayyana cewa gwamnatin tarayya ta fara daukar matakan nemo wasu hanyoyin samar da lantarki ga jihohi arewa.

Adelabu ya ce gwamnatin za ta yi haka domin rage wa mutanen yankin zafin rashin wutar da suke ciki sakamakon lalata layukan dake bawa yankin wutar. 

Ministan ya sanar da hakan bayan ya yi  ganawa da shugaban Nigeria Bola Tinubu a yau Litinin, inda ya ce da farko an so yin amfani da wata karamar tashar bayar da lantarki ta Ikot Ekpene daga Calabar domin kai lantarki yankin arewa, sai dai hakan bai samu ba saboda layin wutar ya lalace.

Adelabu yace suna ci gaba da kokarin gyara layin.

Yace tun a baya a lokacin zaman majalisar zartarwa ta kasa sun nemi ayi gyara a tashar lantarki ta Shiroro wadda itace ke kai wuta yankin Arewa baki daya.

Adelabu ya kara da cewa matsalar ta rashin wuta ta shafi jihohi 17 a fadin arewacin Najeriya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here