An kori dan sanda daga aiki bayan zargin sa da kashe wani mawaki

0
54
police
police

Rundunar yan sandan Nigeria ta sanar da gurfanar da tsohon jami’in ta, mai suna Joseph Ozonwanji da ake zargi da kashe wani mawaki a jihar Enugu.

A sanarwar da ta fitar rundunar ta ce a yanzu jami’in wanda a baya yake aiki a rundunar yaki da kungiyoyin asiri a jihar Enugu, yana tsare a gidan yari bisa tuhumarsa da laifin kisan Okezie Nwamba, wanda aka fi sani da Igbo-Jah.

A jiya Litinin ne aka gurfanar da dan sandan a gaban kotun majistare ta  Enugu ta gabas.

An gufanar da jami’in dan sandan ne bayan da hukumar ‘yansanda ta yi bincike a kansa ta kuma same shi da laifi sannan aka kore shi daga aiki.

Bayan gabatar da tuhumar, mai shari’a Ngozi Edean, ta umarci sashen gabatar da kara ya bayar da shawara kan shari’ar shi kuma wanda ake tuhumar zai yi zaman wakafi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here