An sake kara farashin man fetur a Nigeria

0
109
man fetur
man fetur

Kamfanin mai na NNPCL ya kara farashin litar man fetur a fadin Nigeria, a daidai lokacin da al’umma ke dandana kudar su ta tsadar rayuwa sakamakon karin farashin man da ake samu babu misali.

A yau Talata an hango sabon farashin man zuwa 1,060 akan kowacce Lita a Abuja sai jihar Legas da farashin litar ta koma 1025

Ana kyautata zaton cewa za’a samu tashin farashin man a gidajen man yan kasuwa wanda kafin karin suke siyar dashi akan nair 1150 zuwa 1200.

Idan za’a iya tunawa an kara farashin man a ranar 9 ga watan da muke ciki na Oktoba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here