Dangote yana so a dena shigo da man fetur Nigeria

0
51
Man fetur a Najeriya

Shugaban Matatar man fetur ta Dangote, Aliko Dangote, ya ce za a daina samun dogayen layukan ababen hawa a gidajen mai da zarar dillalan mai sun fara sayen mai daga matatar sa.

Dangote ya bayyana hakan bayan wata ganawa da shugaba Bola Tinubu a yau Talata.

Ya kuma bukaci babban kamfanin man fetur na Najeriya NNPCL, da yan kasuwa su daina shigo da mai daga waje.

Ya ce matatar sa ita ce mafita ga batun dogayen layuka da ake samu a gidajen mai.

Yace zasu iya samar da lita miliyan 30 ko 32 da Nigeria ke bukata a kowacce rana.

Wannan cigaba yazo kasa da wata guda bayan da gwamnatin tarayya ta fara aiwatar da tsarin sayar da danyen man fetur da naira ga Dangote maimakon dala.

Gwamnatin Nigeria ta ce matakin zai daidaita farashin man fetur da kuma karfafa daga darajar naira ta hanyar rage amfani da dala wajen hada-hadar danyen man fetur.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here