Gwamnatin Kano ta amince da naira dubu 71 matsayin mafi karancin albashi

0
54

Gwamnatin Kano ta amince da biyan naira dubu 71 a matsayin mafi karancin albashi ga ma’ aikatan gwamnati.

Gwamna Abba Kabir Yusuf ne ya bayyana hakan a fadar gwamnatin Kano ranar Talata bayan ganawa da wakilan kungiyar kwadago.

Wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X ta ce Karin zai fara aiki ne daga ranar 1 ga watan Nuwamban 2024.

Jihohin Legas da Rivers ne kan gaba a karin albashin wanda suka amince da naira dubu 85,000, sai Neja da zata biya naira dubu 80,000.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here