Manyan Arewa sun kalubalanci shirin Tinubu na kara haraji

0
51

Gwamnoni da sarakunan Arewacin Nigeria sun yi watsi da kudirin dokar kara haraji da Shugaba Tinubu ya aike wa majalisar dokokin kasa.

Sun kalubalanci dokar, musamman maganar karin harajin VAT zuwa 10%, da cewa zai cutar da yankin Arewa da gwamnatocin jihohi.

A wani taro da suka gudanar kan matsalolin da suka dabaibaye Arewa, shugabannin yankin sun buƙaci a gaggauta gyara wutar lantarkin yankin da ta lalace kusan kwanaki 10.

Sun bayyana cewa kwanaki 10 da aka shafe babu wuta a yankin babbar barazana ce ga al’umma da cigaban masana’antu.

Don haka suka bukaci a samar da sabbin layukan tura wuta zuwa yankin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here