Ministan lantarki ya hana karbar kudin wuta a arewa

0
78

Ministan Lantarki, Adebayo Adelabu, ya bayar da tabbacin cewa ba za karbi kudin wuta daga hannun al’ummar Arewacin Nijeriya ba na tsawon lokacin da wutar yankin ta lalace.

Ministan ya sanar da haka ne a lokacin da yake bayar da tabbacin cewa nan da kwana biyar masu zuwa za a dawo da wutar da ta dauke a jihohin Arewa 17.

Da yake jawabi bayan ganawa da Shugaba Tinubu, ministan ya ce zai tattauna da Hukumar Wutar Lantarki da daukacin Kamfanonin Rarraba Wutar Lantarki domin tabbatar da cewa ba a caji yan arewa kudin wutar da ba su sha ba.

Kimanin kwana 10 ke nan babu wuta a jihohi 17 na Arewacin Nijeriya sakamakon lalacewar babban layin lantarkin Shiroro zuwa Kaduna, wanda shi ne ke samar da wutar a Arewa.

Adelabu ya kuma bayyana cewa shugaban kasa Tinubu ya umarci Shugaba Ma’aikatan Fadar Shugaban kasa da Ofishin mai bawa Shugaban Kasa Shawara Kan Harkokin Tsaro su yi duk mai yiwuwa wajen ganin an gyara wutar nan gaba kadan.

Sannan ya ba wa al’ummar Arewa hakuri tare da cewa kamfanin wutar lantarki na Nigeria da hukumomin tsaro suna yin duk mai yiwuwa domin gyara wutar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here