Ba zai yiwu a hukunta talakawa da karin haraji ba—-NDUME

0
68

Sanata Ali Muhammad Ndume, dake wakiltar kudancin Borno a majalisar dattawa, ya nemi gwamnatin tarayya ta dena muzgunawa talakawa da karin haraji.

A yanzu haka majalisun dokokin kasa suna duba yiwuwar amincewa da karin haraji na VAT daga kaso 7.5 zuwa kaso 10 cikin dari, wanda ake zaton zai fara aiki daga farkon shekara mai kamawa.

Sannan akwai zargin a shekarar 2026 za’a kuma kara harajin VAT zuwa kaso 12.5 cikin dari.

Lokacin da yake jawabi a kafar talbijin ta Arise, Ndume yace zai kalubalanci duk wani shirin kara haraji ga talakawa.

Ndume, ya bawa gwamnati shawarar ta rika kara harajin ga masu wadata inda yace a yanzu talakawan Nigeria suna cikin matsalar neman yadda zasu rayu ne, Kuma ba zasu iya jurewa karin harajin ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here