Yan ta’adda sun tarwatsa sansanin sojoji da kauyuka a Niger

0
49

Kauyuka 23 yan bindiga suka tarwatsa tare da sansanin horon sojoji da ke Ƙaramar Hukumar Kontagora a Jihar Neja.

Al’ummar yankin da yan bindigar suka tarwatsa suna cikin filin rundunar sojin a karamar hukumar Kontagora.

Dan Majalisar Dokokin Jihar Neja mai wakiltar Kontagora II, Abdullahi Isah, ya shaida wa majalisar jihar a ranar Talata cewa sansanin horon sojojin ya ratsa kananan hukumomin Kontagora da Mariga.

Isah ya bayyana cewa mutanen yankin da dama suna hannun ’yan bindiga da suka yi garkuwa da su kuma har yanzu ba a sako su ba.Don haka majalisar ta bukaci gwamnatin jihar ta tattauna da hukumomin soji domin kara kokari wajen fatattakar ’yan fashin dajin domin mutane su samu damar komawa gidajensu.

Babban Barikin Sojoji da ke Kontagora babban sansanin soji ne da ke matsayin cibiyar horar da mayakan atilare.

Yan fashin daji sun kafa sansanoni shida a dajin, inda suke barazana ga al’ummar kananan hukumomin Kontagora da Mariga.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here