Dillalan fetur sun ce ba za’a fuskanci karancin mai a Nigeria ba

0
78
man fetur
man fetur

Manyan dillalan man fetur da makamashi sun tabbatar wa da yan Nigeria cewa akwai wadattacen man fetur don haka babu bukatar yan kasa su tayar da hankalin su akan tunanin yiwuwar samun rashin man a nan gaba.

Cikin wata sanarwa da shugaban kungiyar manyan dillalan man, Clement Isong, ya fitar ya ce akwai wadattacen mai a rumbun adana mai na matatar Dangote da kamfanin mai na kasa NNPCL.

Isong ya kuma ce babu wata barazana game da tunanin rasa man ko kuma siya domin boyewa.

Idan za’a iya tunawa a cikin Wannan mako ne kamfanin mai na NNPCL ya kara farashin litar man fetur a fadin kasar nan, wanda hakan ya tabbatar da karuwar farashin a sauran gidajen mai na yan kasuwa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here