Manyan malamai suna so a rika koyar da daliban Nigeria da yaren su

0
45

Masana sun ankarar da mahukunta kan ƙudurinta ta na fara aiki da harsunan cikin gida wajen koyo da koyarwa.

Mahalartan wani taro a kan harsunan Afirka da Jami’ar Ahmadu Bello ta Zaria ta shirya sun kara tunasar da gwamnati a kan kudurinta na amfani da harsunan cikin gida wajen koyar da dalibai a makarantun Nijeriya.

Taron mai taken yadda za a habbaka harsunan Afirka don samar da cigaba ya tattaro masana harsuna daban daban daga sassan Nigeria.Farfesa Ahmed Halliru Amfani, malami a Jami’ar Usmanu Danfodio da ke Sakkwato ya nuna muhimmancin yin amfani da harsunan cikin gida don saukaka fahimtar dalibai tare da cigaban kasa.

Sai dai kuma ya sanar da cewa duk harshen da za a yi amfani da shi dole sai ya kasance yana da cikkakken tsari da tasiri a wajen al’umma.Fafesa Amfani ya ce dole irin wadannan yarurruka su kasance suna da nagartaccen tsarin rubutu da isassun kalmomi.

Farfesa Bello Alhassan na Sashen Harsunan Afirka wanda ya gabatar da jawabi a taron, ya jawo hankali tare nunar da hanyoyin bunkasa harsunan kasashen Afirka sabanin amfanin da hanyoyin baya da suka tsufa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here