Rasha tana neman kamfanin Google ya biya ta tarar kudin da babu su a duniya

0
62

Wata kotun Rasha ta ci tarar kamfanin google saboda takaita wa kafofin yada labaran kasar amfani da dandalin Youtube.

Idan aka kwatanta kudin da dalar Amurka sun kama dala 20,000,000,000,000,000,000,000,000,000,000,000.

Duk da cewa kamfanin na Google na cikin manyan kamfanoni mafiya arziki a duniya, wannan kudi sun zarta arzikinsa da aka kiyasta da cewa yakai dala tiriliyan biyu.

A takaice wannan kudi sun zarta gaba dayan arzikin duniya, da IMF ya ƙiyasta da dala tiriliyan 110.

Kamfanin dillancin labaran Rasha ya ambato kakakin gwamnatin kasar, Dmitry Peskov, duk da cewa ba zai iya ambata wannan adadi ba, amma yana da kyau kamfanin ta mayar da hankali kan wannan hukunci.Kawo yanzu, ba’a ji martanin Kamfanin Google akan hukuncin ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here