Yan ta’adda sun kakabawa al’ummar Zamfara harajin da ba zasu iya biya ba

0
154

Yan ta’adda sun saka harajin naira miliyan goma akan al’ummar garin Faru na karamar hukumar Maradun ta jihar Zamfara, inda suka ce sai sun biya in dai suna son zaman lafiya, ko zuwa aiki gona.

Hakan kari ne kan hare hare da sace mutane da yan bindigar ke yi.Al’amarin ya ta’azzara har mutanen garuruwa shida na yankin sun fara yin kaura zuwa wasu gurare.

Bayanai daga garin na Faru da wasu garuruwa biyar da ke karamar hukumar ta Maradun a jihar Zamfara, sun ce hare hare da sauran masifar da yan bindiga ke yiwa jama’a ta kai makura.

Wani mazaunin garin ya shaida wa BBC cewa suna cikin mummunan yanayi.

Yace ko yaushe kwana suke cikin zullumi.Mutumin wanda ya nemi a sakaya sunan sa ya ce garuruwa shida ne da suka haɗa da Goron Namaye, Janbako, da Faru magami, Ƙaya, da Magami, ke fuskantar kalubalen.

An yi kokarin jin ta bakin gwamnatin jihar ta Zamfara game da wannan batu, amma ba’a yi nasara ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here