An sace matafiya kusan 20 a jihar Niger

0
82

Yan bindiga sun yi garkuwa da matafiya kusan 20 lokacin da suke tafiya a kan hanyar Mariga zuwa Kontagora a Jihar Neja.

Shugaban majalisar dokokin Niger Abdulmalik Sarkin-Daji, ya ce ’yan ta’addan sun sace mutanen dake cikin wasu motoci biyar a ranar Alhamis.

Ya bayyana cewa ’yan ta’addan sun tare hanyar da ta taso daga Baban-Lamba zuwa Beri.

Ya sanar da hakan a martanin da yayi ga rundunar sojin Nijeriya da ta musanta aiwatar da ayyukan ’yan ta’adda a sansanin horon soji da ke kananan hukumomin Kontagora da Mariga.

Shugaban majalisar ya ce iyalan mutanen da aka yi garkuwa da su sun dade suna kaiwa yan ta’addan kudin fansa.

Shugaban majalisar ya bayyana cewa matafiyan da aka sace ranar Alhamis ma an shige da su dajin barikin, wanda ke matsayin sansanin horo ga sojojin rundunar atilare.

Don haka ya bukaci sojoji su bincika don samu sahihan bayanai domin fatattakar bata garin.

Ya kara da cewa maimakon sojoji su tsaya yin ƙorafi da ƙaryata maganar, kamata ya yi su zurfafa bincike su ɗauki matakin da ya dace.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here