Babbar Kotun Tarayya ta ba da belin matasan da aka kama a lokacin zanga zangar tsadar rayuwa a kan Naira miliyan 10 duk mutum daya.
A yau juma’a ne Mai Shari’a Obiora Egwuatu na kotun da ke a Abuja ya kuma ba da umarnin tsare matasan su 76 ’yan kasa da shekaru 18, a gidan yarin Kuje har sai sun cika sharudan belin.
Kotun ta ce wajibi ne wanda duk mai tsaya wa matasan ya kasance babban ma’aikacin Gwamnatin Tarayya da ya mallaki lasisin tuƙi da kuma lambar shaidar zama dan kasa.
Ya kuma sanya 24 ga watan Janairu 2025 a matsayin ranar ci gaba da sauraron shari’ar.
Gwmanatin Tarayya ce ta gurfanar da wadanda suka shiga zanga-zangar tsadar rayuwa da aka gudanar a watan Agusta, 2024 a Jihohin Kano da Kaduna da sauransu, inda take tuhumar suna laifuka 10.