Yan kasuwar arewa sun yi asarar kusan triliyan 2 saboda lalacewar lantarki

0
59
Kayan Abinci

Wasu yan kasuwa a yankin arewacin Nigeria sun ce sun fara tattaro kawunansu don neman diyyar abun da suka yi asarar daga banagaren gwamnatin tarayya sakamakon lalace wutar lantarki ta kusan makonni 2.

Gidauniyar Jino mai rajin kare hakki da fafutukar tabbatar da adalci da shugabanci na gari a Najeriya, ta ce ta fara tattara bayanai na yawan asarar da aka tafka a jihohin da ke yankin 19, don ganin ganin an biya su diyyar wajen rage wa mutane raÉ—aÉ—in asarar da suka tafka, ganin yadda wasu sun durkushe har abada idan ba a kai masu dauki ba, saboda karyewar da jarinsu ya yi baki É—aya.

Shugaban gidauniyar, Imrana Jino ya shaida wa BBC cewar, bai kamata a tsaya kan matakin dawo da wutar lantarkin kaÉ—ai ba, kamata ya yi a haÉ—a da batun biyan diyyar, ko bai wa mutane wani tallafi don ganin sun sake farfaÉ—o da tattalin arzikinsu, da jarinsu.

Jino ya kara da cewa rashin wutar ya gurgunta harkokin lafiya, tare kananan sana’oi da mata ke yi da suke amfani da lantarki waje siyar da kayan sanyi, É“anagren noma duk an sami wannan matsala, musamman masu kiwon kifi, da masu siyar da kajin da ake ajiye su a dakin sanyi.

Shugaban Gidauniyar ta Jino ya ce kawo yanzu ƙiyasin asarar da aka tafka ya kai Naira Triliyan ɗaya da miliyan ɗari biyar, a ɗaukacin fadin jihohin Arewa.

Sannan ya ce suna tattara bayanai, tare da tuntubar lauyoyi, don ganin ta inda za’a fara neman diyyar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here