An fara yada jita jitar mutuwar Sarkin Musulman Nigeria

0
67

Fadar Sarkin Musulman Nijeriya ta yi karin bayani akan jita-jitar da ake yadawa da cewa Sarkin Musulmai mai alfarma Abubakar Sa’ad na III, ya rasu.

Fadar ta yi Allah-wadai da jita-jitar da musanta labarin, inda ta ce Sarkin yana cikin koshin lafiya.

Jami’in hulda da Jama’a na Fadar Sarkin Musulmi, Aminu Haliru ne ya fitar da sanarwar hakan, inda ya ce Masarautar ta yi watsi da maganar, duk da dai kowa ya san kowa zai mutu idan lokaci ya zo.

Tun farko, Shugaba Ƙungiyar MPAC, Disu Kamor ya yi fatali da labarin da ake ta yadawa kan rasuwar.

Kamor ya ce, lafiyar Sarkin Musulmi garau babu abin da yake damun sa a halin yanzu.

Ƙungiyar ta gargaɗi al’umma da su guji yaɗa jita-jita da kuma tantance labari kafin fara yaɗawa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here