Shugaba Tinubu yace babu abinda zai hana shi karawa yan Nigeria haraji

0
73

Shugaban Nigeria Bola Tinubu ya yi fatali da shawarar Majalisar Tattalin Arziki ta kasa (NEC) da ta nemi ya janye aniyar sa ta son kara haraji.

Tun farko dai Ƙungiyar Gwamnonin Arewa ce ta bayyana adawarta ga kudirin inda tace ya ci karo da muradun bukatar yan Arewa.

Yayin da a ranar Alhamis, majalisar tattalin arziki ta kasa ta ba shawarar jingine batun kara harajin.

Sai dai Bayo Onanuga, mai taimakawa shugaban a fannin yada labarai a ranar Juma’a, ya sanar da cewa Tinubu ya nemi majalisar tattalin arzikin kasa da ta bari a aiwatar da sabuwar dokar harajin.

Sanarwar wadda ta yaba wa Majalisar Tattalin Arzikin dangane da shawarar da ta bayar, ta kuma tunatar da ita muhimmancin kara harajin wai domin farfado da tattalin arzikin Nigeria.

Sanarwar ta ce shugaban ya ji korafi da ake yi game da ƙudurin da buƙatar janye shi da ake yi, to sai dai ya ce ƙudirin wanda tuni aka fara muhawara a kansa a majalisar ba za a janye shi ba, sai dai a iya yin wasu gyare gyare.

Tinubu ya ce kudirin da ke gaban majalisa, an aika shi domin kawo gyara a fannin tafiyar da karɓar haraji a kasar Nigeria.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here