Shugaban Nigeria zai rantsar da sabbin ministoci a gobe litinin

0
54
Tinubu
Tinubu

Shugaban Nigeria Bola Tinubu, zai rantsar da sabbin ministocin daya nada a ranar litinin bayan da majalisar dattawa ta kammala tantance su.

Shugaban kasar zai rantsar da su a zauren majalisar zartarwa ta tarayya, dake birnin tarayya Abuja, kamar yadda Bayo Onanuga, mai taimakawa shugaban kasar a fannin yada labarai ya sanar a shafin sa na X, a ranar lahadi.

Wadanda za’a rantsar sun hadar da Nentawe Yilwatda, da Muhammadu Dingyadi sai, Bianca Odumegwu-Ojukwu, da Dr Jumoke Oduwole da Idi Maiha sai Yusuf Ata da Kuma Dr Suwaiba Ahmad.

A ranar 23 ga watan Oktoba ne shugaban kasar ya sauke wasu ministocin sa tare da nada wasu a garambawul din da ya yiwa majalisar zartarwa ta tarayya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here