Tsadar rayuwa ta sanya masu gidan karuwai rufe gidajen su

0
97

Wani bincike ya bayyana yadda tsadar rayuwa da hauhawar farashin kayyakin masarufi ta fara tilastawa masu gidajen karuwar rufe gidajen Sana’ar banzan da suke yi.

Binciken ya nuna cewa an samu raguwar maza masu zuwa gidajen karuwai da otal otal dan yin lalata da mata masu zaman kansu a fadin Nigeria.

Haka ya samo asali akan yadda yanzu abinci yake gagarar mutane ballantana zuwa biyan Kudi domin yin fasikanci.

Daga bangaren masu otal otal din kuwa suna fuskantar karancin kudaden shiga, da kuma tsadar tafiyar da al’amuran su, wanda hakan ya fara tilasta musu daukar matakan dakatar da ayyukan su.

Rahotanni sun tabbatar da cewa wasu matan dake yin mummunar dabi’ar karuwanci sun fara komawa gidajensu su don neman wata hanyar neman kudi tunda wannan ta dauki hanyar durÆ™ushewa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here