Yarabawa sun kalubalanci Tinubu akan fifita kabilar sa

0
57

Kungiyar dake kishin kabilar Yarabawa zalla ta Afenifere ta gargadi Shugaban Nigeria Bola Ahmed Tinubu a kan abin da ta kira son kai da fifita ‘yan kabilar sa ta Yarabawa wajen bayar da mukaman gwamnatin tarayya.

Bayanin ya fito cikin wata sanarwa da shugaban kungiyar Ayo Adebanjo, da kuma sakataren yada labarai na kungiyar Justice Faleye suka fitar a Ibadan, babban birnin jihar Oyo.

Kungiyar ta yi gargadin cewa lamarin zai iya zama barazana ga alaƙar kabilu da kuma zaman tare na lumana a tsakanin kabilun Nigeria.

Afeniferen ta nuna bukatar shugaban ya gyara kuskuren da ta tace ya yi a kan bayar da mukamai ta hanyar son kai.

Afenifere, tace a baya ta kalubalanci irin wannan son kai a Gwamnatin baya, inda tace a yanzu ba zata zuba ido daya daga cikin yayan ta ya rika yin wannan son kai ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here