Fashewar Bom ta hallaka mutane 7 a Borno

0
70

Wani bom daya fashe yayi sanadiyyar mutuwar mutane 7 a kan hanyar zuwa kauyukan Dogon waya, da Masunfanari, a titin Maiduguri zuwa Damboa a jihar Borno.

Mutanen sun gamu da ajalin su bayan da Karamar motar dauko kaya da suke ciki ta taka nakiyar bom din da aka binne, da ake zargin mayakan boko haram ne suka binne nakiyar akan hanya.

Mutane bakwai aka tabbatar sun mutu nan take sai kuma karin wasu da suka jikkata, lokacin da abin ya faru a ranar asabar.

Wani da abin ya faru a gaban idon sa, Bukar Modu, ya sanar da cewa ya kirga gawarwaki bakwai da aka kawo yankin Sulumari da ke daura da unguwar Masinrimari a birnin Maiduguri kafin a yi musu jana’iza.

An yi kokarin jin ta bakin kakakin ’yan sanda jihar Borno, ASP Nahum Kenneth Daso, akan lamarin amma hakan bai samu ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here