Likitocin Kano sun bukaci gwamnati ta kori kwamishinar jihar

0
51

Kungiyar likitoci ta kasa NMA reshen Kano ta bawa gwamnatin jihar wa’adi awanni 48, akan ta kori kwamishinar jinkai Hajiya Amina Abdullahi (HOD) daga mukamin ta kan zargin ta da cin zarafin wata likita mace.

Cikin wata sanarwa da shugaban kungiyar Dr. Abdurrahman Ali, da sakataren sa Dr. Ibrahim D. Muhammad, suka fitar sun ce lamarin ya faru ranar 1 ga watan Nuwamba a sashin bawa kananun yara kulawar gaggawa na asibitin kwararru na Murtala Muhammad.

NMA tace kwamishinar da mukarraban ta da suka hadar da jami’an tsaro sun ci zarafin likitar, inda kungiyar tace likitar tana kula da marasa lafiya sama da dari a lokacin da kwamishinar take neman likitar ta saurare ta.

Dr. Ali, ya bayyana abun da kwamishinar tayi a matsala yin amfani da karfin iko don aiwatar da abin da take so.

Haka zalika NMA tace irin wannan abu da ake zargin kwamishinar da aikatawa ya sabawa dokar aiki, da Kawo wa fannin lafiya nakasu.

Zuwa yanzu ba’a ji martanin gwamnatin Kano akan bukatar da Kungiyar likitocin ta nema ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here