Naira 26 ake siyar da litar man fetur a kasar Iran

0
81
Man Fetur
Man Fetur

Kasar Iran dake yankin gabas ta tsakiya itace kasar da tafi kowacce saukin man fetur a fadin duniya, wanda farashin litar man take akan Dala $0.029 matsayin naira 26.52.

Iran dai tana daya daga cikin Kasashen duniya masu karfin arzikin man fetur, wanda ita kadai zata iya taka rawa wajen karya farashin man ko tashin sa a kasuwar danyen mai ta duniya.

Karanta karin wasu labaran:Dillalan fetur sun ce ba za’a fuskanci karancin mai a Nigeria ba

Daya daga cikin dalilan da suka sanya har yanzu yan kasar Iran ke samun saukin siyan man fetur shine Iran bata yin ma’amala da cibiyoyin bayar da aron kudi na kasashen duniya, wanda suke taka rawa wajen karya tattalin arzikin kasa da jefa ta cikin da na sani.

Haka zalika itama kasar Libya tana siyar da man fetur akan kudin da bai zarce naira 52, ba akan kowacce Lita, saboda shugaban kasar na baya da aka yiwa kisan gilla Moammar Gaddafi, bai bawa turawa damar sace dukiyar kasar ba, sannan baya karbar bashin Turai.

Haka ne ya sanya turawa kitsa yadda aka hallaka Gaddafi, kuma har yanzu kasar ta ki samun zaman lafiya, saboda turawa suna yin amfani da rikicin wajen sace dukiyar kasar.

Sai dai lamarin ba haka yake ba, a kasashe irin su Nigeria wanda suka dogara da kasashen duniya wajen aron kudi, da kuma kin tausayin yan kasar.

A yanzu haka ana siyar da litar man fetur akan farashin 1350, kowacce Lita, wanda abin yafi karfin misali in za’a kwatanta da kasashen Iran ko Libya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here