Babban Hafsan sojojin Nigeria ya mutu

0
53

Babban hafsan sojojin Nigeria Laftanar Kanar Taoreed Lagbaja, ya mutu yana da shekaru 56, a duniya.

Mai taimakawa shugaban kasa Tinubu a fannin tsare tsare da yada labarai Bayo Onanuga, ne ya sanar da hakan.

A kwanakin baya an yada jita jitar mutuwar Lagbaja, amma rundunar sojin ta musanta, inda tace ya tafi kasashen waje domin neman lafiya akan cutar dajin da ta dame shi.

Tun kafin rasuwar tasa shugaban kasa Tinubu ya nada Major General Olufemi Oluyede, a matsayin Mukaddashin babban hafsan sojojin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here