Fashewar Bom ta hallaka mutane 2 a kasuwar jihar Imo

0
67

Wani tashin hankalin fashewar Bom data faru a kasuwar duniya ta Orlu, dake jihar Imo, ta kudancin Nigeria, tayi sanadiyyar mutuwar mutane 2, da jin munanan raunuka ga wasu da dama.

Fashewar ta haifar da firgici ga yan kasuwar, wanda hakan yasa suka shiga zulumi da jiran abun da ka iya tasowa bayan tashin Bom din, wanda ya faru a ranar talata.

Wani shaidar gani da ido ya bayyanawa jaridar Thisday, cewa suna cikin kasuwar kwatsam suka ji tashin hankalin fashewar Bom din da ya sanya mutane gudun neman tsira da rayuwar su, har ta kai ga bom din ya kashe mutanen su biyu.

Mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar Imo Henry Okoye, ya tabbatar da afkuwar lamarin, tare da mutuwar mutane 2 da aka sanar tun da farko.

Sannan ya nemi al’ummar yankin da abin ya faru su kwantar da hankalin su, inda yace suna kan gudanar da bincike.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here