Gwamnatin Kaduna zata bawa masu zanga zangar da aka kama aikin yi

0
50


Gwamnan jihar Kaduna Uba Sani, yayi alkwarin bayar da aikin yi ga matasan jihar da aka kama lokacin zanga zangar kin jinin gurbataccen shugabanci a Nigeria, wadda ta gudana a farkon watan Ogustan shekarar da muke ciki.

Lokacin da yake jawabi ga manema labarai bayan sakin masu zanga zangar yan asalin Kaduna, sakataren gwamnatin jihar Dr. Abdulkadir Mu’azu, yace gwamna Uba Sani, ya umarci cewa a karbi takardun kammala makaranta na wadanda suka kammala gaba da sakandire daga cikin masu zanga zangar.

Uba Sani, yayi alkawarin bawa wasu jarin fara sana’a, wasu za’a basu horon sana’o’in dogaro da kai, sai kuma wadanda za’a dauka aikin gwamnati.

Karanta karin wasu labaran:::Yan ta’adda sun kashe dan takarar Kansila a Kaduna

Amman sakataren gwamnatin yace za’a fara bibiyar halayen masu zanga zangar su 39, don tabbatar da cewa suna da kyakkyawan hali kafin su ci gajiyar wannan alkawari.

Dr. Abdulkadir yace jami’an gwamnati sun karbi bayanan masu zanga zangar, don samun saukin sanin inda suke in an tashi neman su.

An kuma binciki lafiyar su, kafin su shiga cikin al’umma, tare da basu sabbin wayoyin hannu, saboda sun rasa nasu lokacin da aka kama su, tare da bawa kowanne naira dubu dari.

Daga karshe kuma an kai kowanne daga cikin matasan zuwa ga hannun iyayen sa.

Idan za’a iya tunawa an kama masu zanga zangar a farkon watan Ogusta, sakamakon mabanbantan laifukan da ake zargin su da aikatawa ciki har da yunkurin juyin mulki, wanda kotu ta bayar dasu beli kan naira miliyan goma kowanne mutum daya bayan shafe watanni uku a hannun jami’an tsaro.

Matsin lambar da shugaban Nigeria Tinubu, da jam’iyyar sa ta APC suka fuskanta daga yan nigeria ne ya zama sanadiyyar samun nasarar kubutar da yaran, wanda shugaban kasar ya bayar da umarnin gaggauta sakin su bata tare da bata lokaci ba, hakan akayi kuwa wanda tun a ranar talata aka sake su daga gidan yarin kuje dake birnin tarayya Abuja.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here