Kungiyar likitoci zata dakatar da aiki a Kano saboda cin zarafin likita

0
50

Kungiyar likitoci ta kasa NMA reshen jihar Kano ta sanar da shirin ta dakatar ayyukan ta har sai baba ta gani a asibitin kwararru na Murtala Muhammad daga karfe 12 na daren 6 ga watan Nuwamba.

Mai magana da yawun kungiyar reshen Kano, Dr. Muhammad Aminu Musa, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa daya fitar a yammacin yau laraba.

Yace daukar matakin dakatar da aikin nasu ya zo sakamakon yadda gwamnatin jihar ta gaza yin wani abu bayan sun bayar da awanni 48, gwamnati ta dauki mataki akan cin zarafin da suka ce an yiwa wata likita mace a sashin bayar da kulawar gaggawa na asibitin kwararru na Murtala, da ake zargin kwamishinar jinkai Hajiya Amina Abdullahi HOD ta aikata.

Sanarwar ta kara da cewa binciken ma’aikatar lafiya ta jihar Kano ya tabbatar da cewa likitar da abin ya shafa bata da wani laifi.

Tun da farko dai kungiyar NMA ta nemi a kori kwamishinar jinkai Hajiya Amina Abdullahi HOD daga mukamin ta saboda zargin cin zarafin likitar, amma har yanzu gwamnatin Kano bata bayyana matakin zata dauka akan ta ba, bayan gudanar da bincike.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here