Bazan ci amanar Kwankwaso ba—-Gwamnan Kano

0
68

Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf, yace bazai ci amanar mai gidan Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ba.Abba ya bayyana hakan a daren jiya lokacin da ake zantawa dashi kai tsaye ta kafafen yada labarai na Jihar Kano.

Yace Àllah ne ya bashi mulkin Kano, amma Kwankwaso ne silar samun mulkin Kano.

Gwamnan, yana yin wannan jawabi yayin da aka nemi yayi karin haske kan batun sabuwar kungiyar Abba tsaya da kafar ka, dake neman Abba, ya bijirewa umarnin Kwankwaso.

A cewar sa Al’umma Kano ba mutane ne masu butulci ba, dan zai cigaba da yiwa Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, biyayya a matsayin na jagora, kuma a dena batun tsaya da kafar ka.

Haka zalika Abba, ya karyata zargin cewa ya bijirewa kiran wayar Kwankwaso, inda yace ko kadan ba gaskiya a cikin zargin.

A yanzu dai rikicin cikin gida ya mamaye jam’iyyar NNPP reshen jihar Kano, wanda tuni wasu yayan jam’iyyar suka fara nunawa Kwankwaso yatsa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here