Muhimman abubuwan da hirar gwamnan jihar Kano ta daren jiya ta kunsa

0
79

A daren jiya laraba ne gwamna Abba Kabir Yusuf, na jihar Kano ya gabatar da tattaunawa da kafofin yada labarai daban daban na jihar, inda ya yi fashin baki akan al’amuran da suka shafi gwamnatin sa, da Kuma wasu al’amuran siyasa.

A lokacin an kwashe tsawon awanni 2, ana tattaunawar da aka fara tun karfe 10 da dare zuwa 12.

Daga cikin muhimman batutuwan akwai maganar Gwamnatin Kano zata siyo abinci don rabawa al’ummar jihar da manufar rage talaucin da ake ciki.A batun wutar lantarki da ake yawan samun matsalar rashin ta musamman a arewa, Abba yace za’a samar da wutar Solar mai amfani da hasken rana saboda rashin wutar lantarki, ta hanyar tattaunawa da kamfanonin kasashen waje.

Sannan yace ya cika Kaso 65 cikin dari na alkawuran da ya yiwa mutanen Kano, a lokacin yakin neman zabe.Yace wasu daga cikin ayyukan da yayi sun hadar da tituna, gadoji, gyara makarantu, da inganta fannin lafiyaSai batun ruwan sha inda yace sanin kowa ne babu ruwan sha a Kano, tun lokacin mulkin Ganduje, sannan yace gwamnatin Ganduje ta raba filotai akan bututun ruwan da Kwankwaso ya samar, hakan yasa aka gaza samun mafita da sauri akan matsalar rashin ruwan.

Amma yace suna yin bakin kokarin samar da ruwan, musamman rijiyoyin burtsatse da gyara injinan tunkudo ruwa.

Sannan yace jami’an gwamnati sun yi hadin gwiwa da kamfanonin kasar Germany don kawo sabbin injinan tunkudo ruwa masu inganci don samar da ruwan.

Sai maganar taimakawa mata da sana’o’in dogaro da kai, wanda Gwamna Abba yace, za’a cigaba da taimakawa mata da jari na dubu 50, ko 30, don yin karamar Sana’ar dogara da kai.A fannin tsaro kuwa, gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf, yace tun farkon mulkin sa, an samu raguwar ayyukan ta’addanci da rashin tsaro musamman satar wata da dangogin su, wanda hakan ya zama wata babbar masifa a Kano.

Abba yace yayi kokarin ganin an kubutar da kananun yaran da gwamnatin tarayya ta kama, tare da yabawa shugaban Nigeria Bola Tinubu.Sannan yace za’a tabbatar da ingancin lafiyar yaran a asibitin giginyu kafin mikasu ga iyayen su, da kuma taimaka musu da sana’o’in dogaro da kai.Daga batun yan fansho da biyan mafi karancin albashi kuwa gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf, yace ya tsaya tsayin daka wajen magance kalubalen yankan albashin ma’aikata da na yan fansho wanda tsohuwar gwamnatin jihar Kano karkashin Ganduje tayi.

Yace zai yi bakin kakakin sa wajen tabbatar da biyan yan fansho hakkin su akan lokaci da Kuma biyan mafi karancin albashin ma’aikata ba tare da samun matsala ba.Abba, ya kuma ce tsohuwar gwamnatin Ganduje, ta dauko hayar Kamfanonin karbar haraji 120, wanda hakan yake kassara fannin samun kudaden shiga, yana mai cewa daga farkon mulkin sa zuwa yanzu an kori wadancan kamfanoni tare da mayar da su guda 8, don saukaka kashe kudaden gwamnatin a aikin banza.

Daga karshe Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf, yace bazai ci amanar mai gidan Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ba.

Yace Àllah ne ya bashi mulkin Kano, amma Kwankwaso ne silar samun mulkin Kano.Gwamnan, yana yin wannan jawabi yayin da aka nemi yayi karin haske kan batun sabuwar kungiyar Abba tsaya da kafar ka, dake neman Abba, ya bijirewa umarnin Kwankwaso.A cewar sa Al’umma Kano ba mutane ne masu butulci ba, dan zai cigaba da yiwa Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, biyayya a matsayin na jagora, kuma a dena batun tsaya da kafar ka.

Haka zalika Abba, ya karyata zargin cewa ya bijirewa kiran wayar Kwankwaso, inda yace ko kadan ba gaskiya a cikin zargin.A yanzu dai rikicin cikin gida ya mamaye jam’iyyar NNPP reshen jihar Kano, wanda tuni wasu yayan jam’iyyar suka fara nunawa Kwankwaso yatsa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here