Likitocin Kano sun janye yajin aikin da suka fara

0
82
Kano

Kungiyar likitoci ta kasa reshen jahar Kano ta umarci mambobin ta na jihar su koma bakin aiki bayan janye yajin aikin da aka wayi gari da shi a asibitin kwararru na Murtala Muhammad a ranar Alhamis.

Likitocin sun shiga yajin aikin bayan cikar wa’adin sa’o’i 48 da suka baiwa gwamnan Kano,  ya kori kwamishiniyar jin kai, Hajiya Amina Abdullahi HOD, bisa zargin cin zarafin wata likita a asibitin.

Zargin da ta musanta tace ba haka bane.

Duk da cewa yajin aikin bai dauki dogon lokaci ba, amma majinyata sun shiga wani mawuyacin hali a asibitin kwararru na Murtala.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here