An hana jami’an Amotekun zuwa wajen zaben gwamnan jihar Ondo

0
69

Babban Sufeton yan sandan Nigeria Kayode Egbetokun ya haramta wa kungiyar tsaro ta jihohin kudu maso yamma Amotekun da yan Vigilante da sauran makamantan su shiga harkokin zaben gwamnan jihar Ondo.

A wata sanarwa da kakakin rundunar yan sandan Auyiwa Adejobi ya fitar a yau Lahadi, ya ce Babban Sufeton ya bayar da umarnin tura jami’an ‘yan sanda daga sassa daban daban na rundunar domin halartar aikin zaben.

Jam’iyyu 17 ne aka bayyana cewa za su shiga zaben wanda za a yi ranar Asabar mai zuwa, 16 ga watan Nuwamba.

Sanarwar ta ce yan sanda da sauran hukumomin tsaro na gwamnatin tarayya ne za su yi aikin tabbatar da tsaro a lokacin zaben.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here