Shugaban Nigeria ya sauka a kasar Saudi Arabia

0
73

Shugaba Bola Ahmed Tinubu, na Nigeria ya sauka a birnin Riyadh, na kasar Saudi Arabia, a yau Lahadi domin halartar taron koli na kasashen Larabawa da Musulmi da za a fara gudanar wa a gobe Litinin.

Za a yi taron ne bisa gayyatar Sarki Salman da Yarima mai jiran gado, Mohammed bin Salman, bayan makamancin taron da aka yi a shekarar 2023.

Taron zai mayar da hankali kan halin da ake ciki yanzu a Gabas ta Tsakiya.

A sanarwara da mai bai wa shugaban shawara na musamman kan harkokin yada labarai da dabaru, Bayo Onanuga, ya fitar ya ce Tinubu, yana tare da ministan harkokin waje, Yusuf Tuggar, da mai ba shi shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu, da ministan yada labarai da wayar da kan jama’a, Mohammed Idris da kuma shugaban hukumar bayanan sirri ta Najeriya, Mohammed Mohammed.

Sanarwar ta ce ana sa ran a wajen taron Shugaba Tinubu zai gabatar da jawabi a kan rikicin Isra’ila da Falasdinawa, inda zai jaddada matsayar Najeriya ta neman sasanta rikicin ta hanyar dakatar da bude wuta.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here