Sojoji sun kashe manyan yan ta’adda a Kebbi da Zamfara 

0
66
Sojin sama

Rundunar Sojojin Sama ta Nijeriya bangaren atisayen  Fansan Yamma, ta kai hare-haren a wasu ma’ajiyar makamai ta shugaban ‘yan ta’adda Ado Aleiro, tare da kashe mutane da dama a jihohin Kebbi da Zamfara.

Mai magana da yawun rundunar sojin saman Air Commodore Olusola Akinboyewa, ya bayyana cewa hare-haren sun zama wani ɓangare na atisayen Farautar Mujiya, don taimaka wa Sojojin kasa wajen magance laifuka a yankin Arewa maso Yamma.

An kai farmakin a ranar 8 ga Nuwamba, a guraren da suka hadar da sansanin Sangeko a Zamfara, kusa da iyakar Kebbi, da sansanin Aleiro kusa da Asola Hill a Tsafe.

Hare-hare sun lalata manyan wuraren ajiyar makamai na Aleiro tare da raunata manyan mayaƙansa.

Akinboyewa ya tabbatar da cewa hare-haren sun sanya an samu nasarar kubutar da wasu mutane da aka yi garkuwa da su.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here