NNPC ya dena shigo da man fetur Nigeria

0
69

Kamfanin man fetur na NNPCL ya sanar da cewa ya dena siyo man fetur daga kasashen waje don shigo da shi cikin Nigeria.

Shugaban kamfanin NNPCL, Mele Kyari, ne ya sanar da hakan a lokacin gudanar da taron shekara shekara akan harkokin man fetur wanda ya gudana a jihar Legas, a ranar litinin.

Yace daga yanzu NNPCL zai rika siyo man fetur daga Matatar Dangote da sauran matatun cikin Nigeria, tare da jaddada cewa a cikin Nigeria kadai zasu rika siyan tataccen man.

Kyari, ya kuma karyata wasu labaran da ake yadawa masu nuni da cewa kamfanin NNPCL yana yin kafar ungulu ga yunkurin tace man fetur a Nigeria, tare da yiwa harkar tace man zagon kasa, wanda yace sam ba haka bane hasali ma cewa yayi suna farin cikin kasancewa daya daga cikin mutanen dake da hannu a matatar man fetur ta Dangote.

Kafin wannan lokaci an fuskanci rikici tsakanin matatar Dangote da kamfanin NNPCL tun daga batun siyarwa Dangote danyen man fetur, har zuwa amincewa matatar fara siyarwa yan kasuwa man, wanda aka kai ruwa rana har sai da shugaban Nigeria Tinubu ya shiga tsakani.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here