Ruftawar kasa ta kashe masu hakar ma’adanai 13 a Filato

0
54

Kimanin mutane 13 ake tsammani sun mutu bayan ruftawar kasa a wurin hakar ma’adinai na Karamar Hukumar Bassa da ke Jihar Filato.

Mafi yawancin masu hakar ma’adinan da suka rasu matasa ne da basu wuce shekaru 18 zuwa 30 ba.Shugaban karamar hukumar, Bassa Joshua Riti, ya ce mutum bakwai daga cikin wadanda kasar ta afkawa ’yan asalin karamar hukumar ne.

Yace abin takaici ne yanda matasan suka rasa rayuwar su lokacin da suke neman abin da zasu rufawa kansu asiri.

Ya kuma mika ta’aziyyarsa ga iyalai da abokan wadanda abin ya ritsa da su.

Daman a lokaci bayan lokaci ana samun ruftawar kasa akan masu hakar ma’adanai sakamakon rashin kayan aiki na zamani.

Ko a jihohin Niger, da Zamfara, ana samun wadanda Wannan iftila’i ke faruwa akan su.Daman gwamnatin tarayya da gwamnonin wasu jihohin sun haramta hakar ma’adanai ba bisa ka’ida ba, saboda yana taka rawa wajen kara ayyukan ta’addanci.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here