An yi artabu tsakanin Bello Turji da sojojin Nigeria

0
67

An yi musayar wuta ta lokaci mai tsawon tsakanin dakarun sojin Nijeriya da tawagar Bello Turji a garin Gatawa da ke Jihar Sakkwato.

Bello Turji, dai fitaccen dan ta’adda ne daya addabi al’ummar Zamfara da Sokoto.

Rahotanni sun ce tun karfe 6 na safiyar ranar Talata ake jin harbin bindiga a garin har zuwa kusan karfe 3 na yammacin ranar.

Wani shaidar gani da ido ya shaidawa Jaridar Daily Trust cewar ba su taba ganin irin wannan musayar wutar ba, kuma har zuwa lokacin da yake magana ana ta artbau tsakanin bangarorin biyu.

Wannan dai shi ne karon farko da aka ji duriyar Turji tun bayan da aka kashe ubangidansa Halilu sububu da ya gagari yankin Sokoto da Zamfara.

Wannan lamari ya faru bayan bullar sabuwar kungiyar ‘yan ta’adda ta Lakurawa a Kebbi da Sakkwato.Kawo yanzu ba’a samu bayanan adadin wadanda aka kashe a musayar wutar ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here