Hukumar Custom ta tara fiye da kudin da aka ce ta tattara a shekarar 2024

0
58

Hukumar hana fasa kwauri ta Nigeria Custom ta tattara kudin shigar da ya kai naira triliyan 5 da biliyan 9, a cikin Wannan shekara ta 2024, wanda adadin ya zarce abinda aka basu umarnin tattarawa na naira triliyan 5 da biliyan 7.

Shugaban hukumar custom ta Nigeria Adewale Adeniyi, ne ya sanar da hakan a birnin tarayya Abuja ranar talata.

An tattara kudaden ne daga farkon Wannan shekara zuwa jiya, sannan Adewale, yace sun samu karin kaso 10 cikin dari na abinda aka umarci su tattara.

Yace ma’aikatan sa sun kama kayayyakin da aka haramta shigo da su Nigeria da adadin su yakai naira biliyan 28.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here