Gwamnatin Nigeria tana neman Dala biliyan 10, da zata zuba a fannin lantarki

0
46

Gwamnatin tarayyar Nigeria tace tana bukatar kudaden da yawan su yakai dala biliyan 10, don Zuba su a fannin lantarki, daga yanzu zuwa Shekaru 10 masu zuwa, don samun wutar awanni 24 kowacce rana ba tare da daukewa ba.

Gwamnatin tace tana son samun kudin daga bangaren ta da yan kasuwa, kamar yadda ministan lantarki Adebayo Adelabu, ya bayyana lokacin da shugaban Hukumar ICRC, yakai masa ziyarar aiki.

Mai rikon mukamin shugaban sashin hulda da jama’a na ma’aikatar lantarki ta Nigeria Ifeanyi Nwonko, ne ya sanar da hakan cikin wata sanarwa daya aikewa kamfanin dillancin labarai na kasa NAN.

Adelabu, yace gwamnati kadai ba zata iya zubawa fannin lantarki wannan kudi ba, saboda wasu bangarorin masu muhimmanci suma suna bukatar kulawa.

Amman yace sakamakon hadin gwiwa da kamfanoni masu zaman kansu za’a iya samun abin da ake bukata nan da wani lokaci.

Masana harkokin tattalin arziki dai suna ganin cewa adadin kudaden da ake zubawa fannin lantarki a Nigeria da sunan gyaran wuta sun isa ace an kirkiro wata sabuwar lantarkin ko da kuwa ba’a taba samar da ita a kasar ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here