Hukumar tace fina-finai ta jihar Kano ta kai mawaki Rarara gaban kotu

0
67

Hukumar tace fina-finai da Dab’i ta Jahar Kano karkashin jagorancin Abba El-mustapha ta gurfanar da mawaki Dauda Kahutu Rarara a gaban kotu bisa zargin da sakin wata sabuwar waka batare da salewar Hukumar ba.

A wata sanarwa da jami’in yada labarai na Hukumar Abdullahi Sani Sulaiman, ya aikawa da manema labarai ya ce tun kafin wannan lokaci Hukumar tace fina-finai ta aikawa da mawakin sakon korafi dangane da sabuwar wakar daya saki batare da ya kawo an tace ta ba.

Amma mawakin bai bata amsa dangane da korafin data aika masa ba wanda hakan ne dalilin da yasa Hukumar ta garzaya gaban kotu.

Wakilin Hukumar a kotu ya tabbatar da cewa tuni kotun ta aikawa da mawakin takardar gayya ta sammaci sai dia ba’a ga fuskar sa ba a yau 13 ga watan nuwamba a yayin zaman ta.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here